Isa ga babban shafi

Za a fara kafa alamomi don shata kan iyakokin Togo da Ghana

Kasashen Ghana da Togo sun amince da fara aikin kafa alamomi don shata kan iyakar da ta raba kasashe biyu da ke yankin Yammacin Afirka.

Tsaunika dake yankin Kpalimé a Togo.
Tsaunika dake yankin Kpalimé a Togo. CC BY 3.0 /wikimedia Commons/Francois Jake Green (Fanfan)
Talla

Da jimawa shugaban kasar Ghana Nana Akoufo Ado da Shugaban Togo Faure Gnassimbe suka bukaci ganin an kawo karshen wannan matsala da ta shafi kan iyakokin kasashen biyu.

Taswirar kasashen yammacin Afrika
Taswirar kasashen yammacin Afrika © Google Map

An dai share shekaru da dama kasashen biyu na takaddama a game da wannan iyaka,da samun labarin soma aikin kafa alamomi a kan iyakar,wannan tamkar nasara ce a cewar mazauna kan iyakokin kasashen biyu,domin hakan ya taimaka wajen gujewa fada tsakanin Togo da Ghana.

Daga Accra, ga rahoton da wakilinmu Sham’un Abdallah Bako ya aiko mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.