Isa ga babban shafi

RSF ta taimakawa RFI, France 24 wajen cigaba da wanzuwa a Mali ta yanar gizo

Kungiyar kare ‘yancin ‘yan jaridu ta kasa da kasa RSF a takaice ta sanar da samar da wasu hanyoyin yanar gizo, wadanda ke baiwa kafafen yada labaran RFI da France 24 damar ci gaba da isar da shirye-shiryensu da al’ummmar Mali, duk da haramta ayyukansu da gwamnatin mulkin sojan kasar ta Mali suka yi a makon da ya gabata.

Gwamnatin Faransa ta kira dakatarwar da Mali ta yi wa RFI da France 24 a matsayin wani mummunan hari kan ‘yancin ‘yan jarida.
Gwamnatin Faransa ta kira dakatarwar da Mali ta yi wa RFI da France 24 a matsayin wani mummunan hari kan ‘yancin ‘yan jarida. © RFI
Talla

A ranar Larabar da ta gabata ne dai sojojin Mali suka haramtawa kafafen watsa labaran na Faransa watsa shirye-shiryensu a kasar, bisa tuhumarsu da yada rahotannin cewa sojojin sun ci zarafin daruruwan fararen hula.

Sai dai a baya bayan nan, kungiyar kare ‘yancin ‘yan jaridu ta Reporters Without Borders a turance, ta sanar da cewa ta yi amfani da wata fasaharta ta yanar gizo wajen tabbatar da cewa, har yanzu ‘yan Mali za su iya shiga shafukan intanet na gidan rediyon RFI da France24 daga cikin kasar tasu ba tare da wata matsala ba.

Tun a cikin shekarar 2015 ne kungiyar RSF ta fara aiki da irin wannan fasaha domin tabbatar da wanzuwar  shafukan yanar gizo 47 a kasashe 24, ciki har da Rasha, don taimakawa kafafen yada labarai kufcewa kokarin dakile su ba bisa ka’ida ba da gwamnatocinsu ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.