Isa ga babban shafi

Kenyatta ya yi karin kashi 12 kan mafi karancin albashin ma'aikata

Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya sanar da karin mafi karancin albashin kasar da kashi 12 cikin 100 domin taimakawa ma'aikata shawo kan hauhawar farashin kayayyakin masarufi, wanda yakin Rasha da Ukraine ya haddasa.

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta.
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta. REUTERS - SIPHIWE SIBEKO
Talla

Kenyatta ya yi wannan albishir ne cikin wata sanarwa da ofishinsa ya fitar, a ranar Lahadin da ta gabata, a wajen bikin ranar ma'aikata da duniya a Nairobi.

Shugaban ya kara da cewa karin kudin albashin ya zama dole saboda an shafe shekaru 3 ba tare da an sake duba darajar mafi karancin albashi a Kenya ba, a daidai lokacin da tsadar rayuwa ta karu.

Kafin karin da aka yi dai, mafi karancin albashin ma’aikata a Kenya ya kama ‘shillings 13,500’ kwatankwacin dala 116.68 kowane wata, wato naira dubu 48 a kudin Najeriya.

Uhuru Kenyatta.
Uhuru Kenyatta. REUTERS - MONICAH MWANGI

Kamar yadda yake a sauran kasashe dai suma ‘yan kasar Kenya na kokawa da hauhawar farashin kayayyakin masarufi, da suka hada da man girki da man fetur, sakamakon mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine daga ranar 24 ga Fabrairu.

Hukumar kididdiga ta kasar ta ce hauhawar farashin kayayyaki a Kenya da ke gabashin Afirka ya rika karuwa sannu a hankali zuwa kashi 6.47 daga kashi 5.56 cikin 100 a watan Maris.

A watan da ya gabata, kasar ta fuskanci karancin mai, inda zirga-zirgar ababen hawa a wasu sassan birnin Nairobi ta tsaya cak, yayin da masu ababen hawa ke shiga dogayen layukan da ke wajen gidajen mai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.