Isa ga babban shafi
Guinea - Juyin mulki

'Yan adawar Guinea sun yi watsi da shirin mulkin Soji na watanni 36

Manyan jam’iyyun adawa a Guinea sun yi watsi da bukatar da sojoji suka gabatar na basu damar ci gaba da mulki har zuwa nan da watanni 36 gabanin gudanar da zabe a kasar.

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kanal Mamady Dambouya, bayan wata ganawa da wakilin kungiyar ECOWAS a birnin Conakry.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kanal Mamady Dambouya, bayan wata ganawa da wakilin kungiyar ECOWAS a birnin Conakry. AFP - JOHN WESSELS
Talla

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da hadakar jam'iyyun adawar Guinea 3 suka fitar da goyon bayan kananun jam'iyyu da ke mara musu baya sun bayyana rashin amincewarsu da matakin tare da bukatar gaggauta gudanar da zabe a kasar ta yammacin Afrika.

Tuni dai majalisar dokokin rikon kwaryar Guinea, ta amince da bukatar da sojojin suka mika mata wanda ke nufin sai nan da shekaru 3 masu zuwa za a gudanar da zabukan dimokuradiyya a kasar.

Da farko dai shugaban sojojin da suka kwaci mulki a kasar Kanar Mamady Doumbouya, ya nemi a ba shi watanni 39 ne to amma ‘yan majalisar suka rage watanni uku.

A watan Satumban bara ne sojojin na Guinea karkashin jagorancin Kanal Mamay Doumbouya suka yi juyin mulki a kasar sakamakon tabarbarewar al’amura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.