Isa ga babban shafi
Zaben Somalia

Aminan Somalia sun yi lale marhabin da sabon shugaban kasar

Abokan huldar kasa da kasa na Somalia sun yi maraba da zaben sabon shugaban kasar Hassan Sheikh Mohamud, wanda ya hau karagar mulki bayan shafe tsawon watanni ana fama da tashe-tashen hankula da suka hada da na masu tayar da kayar baya, da kuma fari mai muni.

Sabon shugaban Somalia, Hassan Cheikh Mohamoud.
Sabon shugaban Somalia, Hassan Cheikh Mohamoud. REUTERS - Ismail Taxta
Talla

Mazauna Mogadishu babban birnin kasar sun yi ta tsere kan tituna suna buga gwangwani na karafa tare da harba bindigogi sama suna murna yayin da aka sanar da sakamakon zaben.

Masana dai na ganin cewa kalubalen da ke gaban shugaban sun kunshi matsalar yunwa da fari ya haifar, kuma sabon shugaban zai kuma bukaci a gyara barnar da aka shafe watanni ana gwabzawa a siyasance, a matakin zartarwa da kuma tsakanin gwamnatin tsakiya da hukumomin jihohi.

Kasar da ke fama da matsalar  lamuni tana cikin hadarin rasa damar samun tallafin dalar Amurka miliyan 400 daga Asusun Ba da Lamuni na Duniya.

A farkon watan nan ne dai wani hari da aka kai kan sansanonin kungiyar tarayyar Afrika AU ya yi sanadiyar mutuwar dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Burundi 10 a cewar rundunar sojin kasar. Wannan dai shi ne hari mafi muni da aka kai wa dakarun AU a kasar tun shekara ta 2015.

Wasu tagwayen hare-haren kunar bakin wake da aka kai a watan Maris sun kuma kashe mutane 48 a tsakiyar Somaliya, ciki har da wasu 'yan majalisar dokokin kasar biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.