Isa ga babban shafi

Kamaru na bikin cika shekaru 50 da dunkulewa zuwa kasa guda

A yau juma’a ake gudanar da bukukuwa cika shekaru 50 da kada kuri’ar amincewa da kawo karshen tsarin tarayya a Kamaru, tare hadewar bangaren gabashi da yammacin kasar a matsayin kasa guda dunkulalliya.

Shugaba Paul Biya na Kamaru.
Shugaba Paul Biya na Kamaru. REUTERS/Mike Segar
Talla

Kafin ranar 20 ga watan mayun shekarar 1972 dai, Kamaru na rayuwa ne a karkashin tsarin tarayya, wanda ya hada Yankin Gabashi da galibinsa na magana ne da harshen faransanci, yayinda ake amfani da turancin ingilishi a bangaren yamma.

An dai bayyana ranar ta yau a matsayin ta hadin kai a tsakanin al’ummar kasar, inda ake gudanar da gagarumin biki ciki har da shirya faretin sojoji da fararen hula a birnin Yaounde fadar gwamnatin kasar.

Bikin dai na zuwa ne a cikin wani yanayi na zaman tankiya sakamakon rikicin rikicin da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Kasar da kuma Kudu maso Yammacin kasar da ke fama da ‘yan bindiga da ke neman ballewa don samar da ‘yantacciyar kasar mai suna Ambazonia.

Wasu daga mazaunan yankunan da ke amfani da turancin ingilishi dai na zargin cewa gwamnatin tsakiya da ke Yaounde, ta karya alkawarran da aka daukarwa jama’arsu kafin amincewa da kawo karshen tsarin tarayya, kuma wannan ne dalilin rashin samun fahimta a tsakaninsu da gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.