Isa ga babban shafi

Mun shirya tsaf don gurfanar da Jammeh a gaban kotu - Gambia

Gwamnatin Gambia ta ce a shirye take ta gurfanar da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh a gaban kotu, a bisa tuhumarsa da aikata laifuka da dama a tsawon shekaru sama da 20 da ya shafe yana mulkin.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh.
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh. AP - Jerome Delay
Talla

Cikin sanarwar da ta fitar, ma’aikatar shari’ar Gambia ta bayyana amincewa da shawarwari guda 265 da kwamitin tantance gaskiya, da sulhu na TRRC, wadda gwamnatin kasar ta kafa ya bayar, musamman akan tuhumar tsohon shugaban kasa Yahya Jammeh da laifuka da dama da aka aikata a zamanin mulkinsa, tsakanin shekarar 1994 zuwa 2017.

Kwamitin na tantance ta gaskiya ya gano cewa mutane 240 zuwa 250, ciki har da ‘dan jarida kuma wakilin AFP Deyda Hydara, aka kashe a zamanin mulkin tsohon shugaban na Gambia.

Kididdiga ta nuna cewar, tun bayan kafa kwamitin a shekarar  2017, mambobinsa sun saurari jawabai daga mutane kusan 400 a matsayin shaidu kan zarge-zargen da ake yi wa Jammhe, kafin su karkare zamansu a watan Mayu na shekarar 2021.

Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh, yayin da yake barin birnin Banjul bayan tilasta masa sauka daga mulki.
Tsohon shugaban Gambia Yahya Jammeh, yayin da yake barin birnin Banjul bayan tilasta masa sauka daga mulki. AP - Jerome Delay

Yahya Jammeh yayi gudun hijira

Yanzu haka dai tsohon shugaba Jammeh na gudun hijira a kasar Equatorial Guinea, wadda ba ta da wata yarjejeniya ta mika masu laifi ga Gambia.

A wani taron menama labarai, ministan shari’a Dawda Jallow ya ce zai samar da ofishin mai gabatar da kara na musamman da kuma kotu ta musamman a Gambia, domin sauraron shari’ar tsohon shugaba Jammeh da tsaffin mukarraban gwamnatinsa da ke tuhuma.

Masu fafutukar kare hakkin bil adama na zargin Jammeh, wanda ya cika shekaru 57 a duniya a ranar Laraba, da aikata laifuka da dama ciki har da, kafa gungun masu halaka mutanen da yake kallo a matsayin barazana da kuma yi wa wata sarauniya kyau fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.