Isa ga babban shafi

An sace sojojinmu biyu a Jamhuriyar Congo - Rwanda

Kasar Rwanda ta ce ‘yan tawaye sun sace biyu daga cikin sojojinta a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Cango.

Wasu sojojin kasar Rwanda.
Wasu sojojin kasar Rwanda. © REUTERS/Jean Bizimana/File Photo
Talla

Lamarin ya zo ne bayan da gwamnatin Jamhuriyar Congon ta gayyaci jakadan Rwanda tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a tsakaninsu, a bisa zargin kasar ta Rwanda da goyon bayan kungiyar 'yan tawayen M23 da ke kai hare-hare a yankinta na gabas.

A makon da ya kare fada ya barke tsakanin dakarun Congo da mayakan M23 a bangarori da dama a arewacin Kivu, lardin dake gabashin jamhuriyar ta Congo mai fama da rikici, wanda ya yi iyaka da kasar Rwanda.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta ce rikicin ya raba mutane akalla dubu 72,000 da muhallansu, inda ta yi gargadin cewa wadanda ke gudun hijira na fuskantar tashin hankali da kuma hasarar dukiyar da ake sace musu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.