An kashe mutane 20 a harin Congo
Akalla mutane 20 ne aka kashe a wani sabon tashin hankali da ya auku a lardin Ituri da ke gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, abin da ake zargin mayakan ADF da suka yi kaurin-suna ne suka kaddamar da harin.
Wallafawa ranar:
An kai harin ne cikin dare a kauyen Bwanasura da ke yankin Irumu, kamar yadda hukumomi a yankin Kivu suka bayyana a shafin Twitter.
Ituri da lardin Kivu ta Arewa na fama da hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai, wadanda yawancinsu suka yada zango a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango.
Hukumar Tsaron Kasar ta ce ana zargin kungiyar ADF da ke ikrarin jihadi da alhakin kai harin.
Ko da yake an kai wa ADF hari a wani farmakin hadin gwiwa da dakarun gwamnati da na Uganda suka kaddamar a watan Nuwambar bara bayan hare-haren bama-bamai a Kampala babban birnin kasar ta Uganda.
A cikin watan Maris, akalla mutane 30 ne ake zargin 'yan tawayen suka kashe a Arewacin Kivu sannan sama da mutane 50 ne suka mutu a wani hari na kwanaki biyu da suka kai kauyukan Irumu.
Ana zargin kungiyar ADF da aikata kisan kiyashi, sace-sace, inda aka yi kiyasta adadin rayukan da ta kashe ya kai dubbai a kasar.
Tun daga watan Afrilun 2019, wasu hare-haren da aka kaddamar a gabashin kasar, ADF ta dauki alhakin kaiwa, kuma tuni kungiyar IS, ta bayyana kungiyar a matsayin reshenta da ke yankin tsakiyar Afirka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu