Isa ga babban shafi

Akwai yiyuwar kungiyar kasashen ECOWAS za ta sassauta wa Mali takunkuman ta -Sall

Shugaban Senegal Macky Sall da ke matsayin shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, ya ce akwai yiyuwar kasashen Yammacin Afirka za su sassauta wa Mali takunkuman da suka kakaba ma ta bayan da sojoji suka yi juyin mulki har sau biyu.

Macky Sall, Shugaban kasar Senegal ya yi tattaunawa da France 24 da RFI
Macky Sall, Shugaban kasar Senegal ya yi tattaunawa da France 24 da RFI © RFI/France 24
Talla

Shugaban kasar ta Senegal Macky Sall ya ce tabbas, sabon jadawalin da mahukuntan kasar suka gabatar da cewa za su mika mulki a hannun gwamnatin fararar hular a watan maris na 2024, shawara ce da tuni shugaban mai shiga tsakanin na Ecowas ya gabatar da taron shugabannin kasashen wanda ya gudanar a birnin Accra.

Wannan shawara ce da mai shiga tsakani na kungiyar Ecowas ya gabatar wa taron shugabannin kasashen yankin, inda yake cewa rikon kwaryar zai share tsawon watanni 24 ne amma daga watan maris na shekara ta 2021 amma karkashin wasu sharuda da aka gindaya.

Shugaba Macky Sall ya jaddada cewa sun tafka doguwar mahawara game da wannan batu, inda daga bisani muka sanar da  manzon Ecowas cewa ba za mu iya daukar mataki ba a wannan taro, amma zai iya ci gaba da kokari a cikin wata daya mai zuwa domin samun cikakken bayani daga mahukuntan Mali dangane da yadda jadawalin zabukan zai kasance.

A  bangare Shugabanin kasashen ECOWAS sun dau alkawarin cewa ranar 3 ga watan gobe na yuli ne za su sake zama domin daukar matakin karshe. Tabbas akwai alamun cewa an samu ci gaba amma ba za su tabbatar da hakan ba sai a watan yuli mai zuwa.

Matukar suka cika sharuddan da aka gindaya musu, to Ecowas za ta cire wadannan takunkumai da ke haddasa tarin matsaloli ga al’ummar kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.