Isa ga babban shafi

Morocco ta haramta nuna fim "The Lady of Heaven" a kasar

Kasar Morocco ta haramta nuna wani fim  daga dan kasar Birtaniya mai suna The Lady of Heaven,fim dake a matsayin batanci ga addinin musulunci  a cewar hukumomin kasar ta Morocco.

Fim The Lady of Heaven
Fim The Lady of Heaven © TWITTER
Talla

Fim "the lady of Heaven" da wani dan kasar Birtaniya mai suna Eli King  tare da hadin gwiwar Yasser Al Habib suka shirya  na yo dubi ne kan daya daga cikin 'yayan mai cira da aminci Allah su tabbata a gareshi  Fatima Zahra.

Fim The Lady of Heaven
Fim The Lady of Heaven © TWITTER

Hukumar sa ido dama tsara fina-finai ta kasar ta Morocco ce ta fitar da sanarwar haramta wannan fim  a fadin ksar,kazzalika babbar hukumar dake jagoranatar addinai a kasar ta haramta nuna wannan fim a fadin kasar ta Morocco.

Ranar 3 ga watan yuni ne aka yada wani Fim karo na farko a Birtaniya,wasu kasashe da suka hada da Pakistan,Masar,Irak,Iran dukkanin su sun haramta nuna wannan fim a kasashen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.