Isa ga babban shafi

Afrika na bukatar kashe dala biliyan 25 don wadatuwa da lantarki- IEA

Hukuma dake kula da makamashi ta Duniya ta ce nahiyar Africa na bukatar dala biliyan 25 don samar da wutar lantarkin da zata wadaci al’ummar Nahiyar cikin shekara guda.

Karancin lantarki na ci gaba da kasancewa babbar matsala ga tattalin arzikin nahiyar Afrika.
Karancin lantarki na ci gaba da kasancewa babbar matsala ga tattalin arzikin nahiyar Afrika. REUTERS/Ina Fassbender
Talla

A cewar hukumar nan da shekarar 2030 akwai bukatar wutar lantarki ta wadaci al’ummar nahiyar Africa, la’akari da yadda adadin masu samun wutar a Nahiyar Africa ke kara raguwa.

Hukumar ta yi karin bayanin cewa mutane miliyan 600 dai-dai da kaso 43 cikin dari na al’ummar Nahiyar Africa ke fama da karancin wutar lantarki, musamman a yankin Sahara.

A cewar hukumar adadin ya karu da kaso 4 cikin dari wato yawan miliyan 25, idan aka kwatanta da shekarun 2019 zuwa 2021.

Hukumar ta IEA ta ce yakin Ukraine da Russia ya kara ta’azzara rashin wuta a Nahiyar Africa, saboda karancin makamashi a duniya da yakin ya haddasa, baya ga tasirin Covid-19 da dama ake fama da shi.

Sai dai hukumar ta ce da gwamnatocin kasashen Africa zasu hada kai tare da tayar da dala biliyan 25 to da bala’in karancin wutar lantarkin zai saukaka kwarai da gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.