Isa ga babban shafi

Sojojin Mali sun yi luguden wuta kan 'yan ta'adda a tsakiyar kasar

Rundunar sojin Mali ta ce dakarunta sun kai hare-hare ta sama kan mayaka masu ikirarin jihadi ‘ya’yan kungiyar ‘Macina Katiba’ mai biyayya ga Al-Qa’eda dake tsakiyar kasar, biyo bayan kisan gillar da aka yi wa fararen hula akalla 132.

Wani sojan Mali a wajen garin Sevare mai fama da matsalar tsaro.
Wani sojan Mali a wajen garin Sevare mai fama da matsalar tsaro. AP - Thibault Camus
Talla

A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, ta ce ta kai hare-haren ne a tsakanin ranakun Litinin zuwa Laraba a kusa da Bankass da Segue, wadanda ke gaf da yankin da aka tafka ta’asar kashe fararen hular fiye da 130.

Sojojin na Mali dai basu yi karin bayani akan hare-haren da suka kaiwa ‘yan ta’addan ba, zalika babu wata majiya  da ta tabbatar da hakan.

Kasar Mali ta fuskanci daya daga cikin kisan fararen hula mafi muni a karshen mako, wanda shi ne na baya bayan nan a jerin kisan kiyashin da ake ci gaba da yi a yankin Sahel.

Mutane da dama sun yi zanga-zangar neman kariya daga gwamnatin Mali

Majalisar Dinkin Duniya da Faransa da sauran masu sa ido na kasa da kasa suna cigaba da bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar tsaro a kasar Mali.

Fararen hula da dama ne suka yi zanga zanga ranar Talata a Bankass domin neman kariya daga gwamnati.

Tun daga shekarar 2012 kasar Mali ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin jihadi.

Tashin hankalin ya fara ne daga arewacin kasar ta Mali, daga bisani kuma ya bazu zuwa yankin tsakiya da kuma  kasashe makwafta da suka hada da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.