Isa ga babban shafi

Za a gudanar da zaben Mali nan da shekaru biyu masu zuwa

Majalisar Sojin Mali ta fitar da wani sabon jadawali dake kayyade  cewa za a gudanar da zaben shugaban kasar a watan  fabarirun shekarar 2024,sanarawr dake zuwa kasa da kwanaki uku kafin a gudanar da taron kungiyar Ecowas.

shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita.
shugaban gwamnatin sojin Mali Assimi Goita. © AFP
Talla

Sanarwar na zuwa ne yayin da suka rage kwanaki uku kasashen yammacin Afirka a karkashin inuwar kungiyar Ecowas su gudanar da taron su  a Accra na kasar Ghana da nufin dubba yiyuwar cirewa kasar takukunman da aka kakkaba mata tun bayan juyin mulki.

Hukumomin sojin kasar ta Mali sun tsaida watan Fabarairu shekarar 2024 a matsayin watan da za a gudanar da zaben shugaban kasar,watan Maris na shekara ta 2023 watan da za a gudanar da zaben raba gardama ko na  jin ra’ayin mutan kasar dangane da sabon kudin tsarin mulkin kasar ta Mali.

Ta bakin daya daga cikin manyan hafsan soja kasar ta Mali,kanal Abdoulaye Maiga mai mukamin Ministan  cikin gidan kasar ta Mali,hukumomin sojin kasar na iya kokarin su na ganin sun dawo da kasar sahun kasashe da ake damawa da  su a bangarori da suka jibanci tattalin arziki,siyasar Duniya.

Jami’in ya bayyana cewa ,cimma  wannan mataki  tare da bayyana wannan jadawali da ya shafi zabe kasar ta Mali ,na nuni cewa hukumomin sojin dake rike da madafan iko da gaske suke wajen ganin mulki ya koma hannun farrar hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.