Isa ga babban shafi

Dakarun kasashen EU sun kawo karshen yaki da ta'addanci a Mali

Ma’aikatar tsaron Faransa ta sanar da kawo karshen aikin rundunar sojin hadin gwiwa wadda aka kafa a shekara ta 2020 don yaki da ta’addanci a yankin Sahel da ake kira Takuba.

Daya daga cikin sansanonin sojin kasashen Turai a kasar Mali.
Daya daga cikin sansanonin sojin kasashen Turai a kasar Mali. © AFP - DAPHNE BENOIT
Talla

Ma’aikatar tsaron Faransa ta ce, rundunar ta kunshi zaratan dakaru na musamman har 800 daga kasashen Faransa, Belgium, Italiya, Estonia, Hungary, Netherlands, Portugal da kuma Sweden, wanda tuni sojojin dake cikin ayarin karshe na rundunar suka koma kasashe a 30 ga watan jiya.

Wannan dai na daga cikin jerin alkawurran da shugaba Emmanuel Macron ya dauka lokacin da yake sanar da janyewar dakarun Barkhane daga Mali biyo bayan sabanin da aka samu tsakanin Faransa da gwamnatin mulkin sojin kasar.

Kakakin ma’aikatar tsaron Faransa Janar Pascal Ianni, tun da farko an kafa rundunar Takuba domin yin aiki kafada-da-kafada da sojojin Mali, yayin da a hannu daya dakarun rundunar ke da ‘yanci kai farmaki kan maboyar ‘yan ta’adda a duk lokacin da bukatar hakan ta taso.

Bayanai sun ce yanzu haka ana kan tattaunawa tsakanin kasashen Turai da kuma mahukuntan Jamhuriyar Nijar, domin duba yiwuwar kafa sabuwar allakar soji tsakanin bangarorin biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.