Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen Rwanda da Congo za su zauna a teburin sulhu

A wani mataki na warware tsamin dangantaka tsakanin kasashen Rwanda da jamhuriyar Demokradiyar Kwango masu makwabtaka da juna, mai shiga tsakani wato kasar Angola tace shugabannin kasashen biyu sun amince ayi wata tattaunawa a Luanda cikin wannan mako.

Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame tare da Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila
Shugaban kasar Rwanda, Paul Kagame tare da Shugaban kasar Jamhuriyyar Congo Joseph Kabila © AP
Talla

Sanarwar da fadar gwamnatin Angola ta fitar ta ce a wannan Laraba ake sa-ran Shugaban Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Jamhuriyar Demokradiyar Congo Felix Tshisekedi za su gana a babban birnin kasar dake gabar tekun kudancin Afirka.

Shugaban kasar Angola Joao Lourenco, babban mai shiga tsakanin kasashen dake yankin Tafkin Congo, zai yi kokarin sulhunta bangarorin biyu dake nunawa juna yatsa bisa zargin yiwa juna makarkashiya.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da Demokradiyar Congo mai arzikin ma'adinai ke fafutukar ganin ta dakile dimbin kungiyoyin da ke dauke da makamai a gabashin kasar.

Kazamin rikicin ‘Yan tawaye na baya-bayan nan ya sake farfado da dadaddiyar gaba na shekaru da dama tsakanin Kinshasa da Kigali, yayin da Congo ta zargi Rwanda da taimakawa mayakan M23.

Kasar Rwanda ta sha musanta goyon bayan 'yan tawayen, yayin da kasashen biyu ke zargin juna da kai hare-hare a kan iyakokisu

A farkon wannan watan ne kasashe da dama suka amince da kafa wata runduna ta yankin don taimakawa wajen kawo karshen tashin hankalin.

Lourenco a watan Mayu ya kulla yarjejeniyar sakin sojojin Rwanda biyu da aka kama a yankin Jamhuriyar dimokradiyyar Kwango.

A lokacin ofishinsa ya ce an cimma matsaya kan ganawar shugabannin biyu ido da ido a Luanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.