Isa ga babban shafi

Sojin Congo sun dakile harin 'yan tawaye a gidan yarin gabashin kasar

Dakarun Jamhuriyar dimokaradiyyar Congop sun dakile wani hari da ‘yan tawaye suka kai wani gidan yari a gabashin kasar, kamar yadda rundunar sojin kasar ta bayyna a yau Asabar, bayan wani kazamin hari a farkon wannan makon.

Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a garin Beni.
Sojojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a garin Beni. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Rundunar sojin kasar ta ce ‘yan tawayen kungiyar ADF ne suka afka wa gidan yarin garin Beni da ke arewacin yankin Kivu, inda yaki ya daidaita a ranar Juma’a.

Rundunar sojin ta ce maharan sun kai harin ne da zummar ceto manyan kwamandojinsu da ke tsare, amma kuma abin ya faskara.

Ko a daren Alhamis, sai da ‘yan tawayen na ADF suka kai kazamin hari a garin Beni a cikin dare, lamarin da ya lakume rayukan fararen hul 6.

Kungiyar ‘yan tawayen  ADF,  wadda kungiyar IS ke ikirarin cewa wani bangare na ta ne na  yankin Tsakiyar Afrika tana daga cikin mafi aikata kisa daga cikin sama da kungiyoyi masu daukar makamai da ke yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.