Isa ga babban shafi

Fasinjojin jirgin sama sun auna arziki bayan sun yi hatsari

Wani jirgin fasinja dauke da mutane 30 ya fadi dai-dai lokacin da yake shirin sauka a filin jiragen sama na Mogadishu babban birnin kasar Somalia, amma babu wanda ya rasa ransa.

Jirgin Jubba Airways da ya yi hatsari a Somalia
Jirgin Jubba Airways da ya yi hatsari a Somalia © SparkChronicle
Talla

Sai dai kuma babu wanda ya rasa ransa cikin dukannin mutane 30 din da ke cikin jirgin, da wani fai-fan bidiyo da ya rika yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yadda jirgin ya tuntsire, a kokarin da yake yi na saukar gaggawa.

Bakin hayaki ya turnuke sararin samaniya, yayin da masu aikin kashe gobara suka fara aiki cikin gaggawa don kashe wutar da ta tashi a jirgin, lokaci guda kuma ana kokarin zakulo mutanen cikin jirgin.

Bayanai na cewa tuni aka garzaya da fasinjojin asibiti don ba su agajin gaggawa, yayin da aka fara tattara bayanan dalilin saukar gaggawar jirgin.

Jirgin na Jubba Airways ya taso ne daga garin Baidoa zuwa babban birnin kasar Mogadishu, kafin ya yi hadarin a filin jirgin saman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.