Isa ga babban shafi

Emmanuel Macron na ziyara a wasu kasashen Afirka ciki harda Kamaru

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya fara wani rangadi zuwa wasu kasashe uku na yammacin Afirka a ranar Litinin a ziyarar farko da zai kai nahiyar tun bayan sake zaben sa a wani wa’adi na biyu, a wani mataki na neman sake farfado da alakar Faransa da kasashen da ta yi wa mulkin mallaka.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron lokacin da yake barin Paris domin rangadi wasu kasashen Afirka, 25/07/22.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron lokacin da yake barin Paris domin rangadi wasu kasashen Afirka, 25/07/22. © AP/Gonzalo Fuentes
Talla

Macron zai fara rangadin nasa ne daga ranar Litinin 25 zuwa 28 ga watan Yuli, wanda kuma shine karo na farko a wajen Turai na sabon wa'adinsa, inda zai fara da ziyara zuwa kasar Kamaru, kafin ya wuce Benin, sannan ya kammala ziyarar a kasar Guinea-Bissau.

Ajanda

Babban ajandar tattaunawar dai ita ce batun samar da abinci, inda kasashen Afirka ke fargabar karancin hatsi musamman wanda mamayewar da Rasha ta yi wa Ukraine ya haifar.

Sai dai kuma batun tsaro zai dauki hankali a daidai lokacin da Faransa ke shirin kammala janyewarta daga Mali a bana, inda daukacin kasashen yankin ke neman kawar da fargabar hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi.

Ziyarar zuwa kasashe uku da ba kasafai shugabannin duniya ke zuwa ba, na zuwa ne bayan da Macron ya lashe wani sabon wa'adi a watan Afrilu, inda ya yi alkawarin ci gaba da kokarin kulla sabuwar alaka tsakanin Faransa da Afirka.

Gasa

Faransa ta damu da yadda wasu manyan kasashen duniya da ke neman gindin zama a yankin da har yanzu take gani ita tafi dacewa a ciki, musamman Turkiyya karkashin Shugaba Recep Tayyip Erdogan da kuma China da Rasha.

'Mafi fifikon siyasa'

Ziyarar "za ta nuna irin jajircewar shugaban kasar wajen sabunta alaka da nahiyar Afirka", in ji wani jami'in fadar shugaban kasar Faransa.

A kasar Kamaru da ke fama da rikicin kabilanci da kuma tada kayar bayan 'yan awaren anglophone, Macron zai gana da shugaba Paul Biya mai shekaru 89, wanda ya shafe kusan shekaru 40 yana mulkin kasar kuma shi ne shugaba mafi dadewa da ba na sarauta ba a duniya.

Dangane da wannan ziyara mun tattauna da Bashir Ladan, wani dan Jarida a Kamaru kuma mai bibiyar harkokin siyasar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.