Isa ga babban shafi

An yi wa Majalisar Dinkin Duniya bore a Congo

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi wa ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Goma a gabashin Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo tsinke, lamarin da ya sanya aka kwashe jami’an da ke ofishin a jiragen sama masu saukar ungulu.

Wasu daga cikin masu neman tabbatar da zaman lafiya a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo
Wasu daga cikin masu neman tabbatar da zaman lafiya a Jamhuriyar Demokuradiyar Congo © Guerchom Ndebo / AFP
Talla

Masu zanga-zangar da ke rera wakokin kin jinin Majalisar Dinkin Duniya, sun balle ofishin wanzar da zaman lafiya na Majalisar da ke birnin Goma, tare da yin awon gaba da wasu kayayyaki, a kokarinsu na neman su fice daga kasar.

Daya daga cikin masu zanga-zanga ya ce,

Fiye da shekara 20 ke nan sojojin nan, na cikin kasarmu, amma ba mu ga wani abu da suka yi ba. Muna bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta kwashe su daga kasarmu, domin ba mu ga amfanin su ba”.

 

Sojojin wanzar da zaman lafiya da ke Jamhuriyar Dimukaradiyar Congo da ake kira da MONUSCO, na fuskantar suka ne a ko da yaushe bayan da suka gaza dakatar da rikici a gabashin kasar, kamar yadda wani daga cikin masu zanga-zangar ya bayyana, yana mai cewa,

Wadannan jami’an tsaron ya kamata su hada hannu wajen aiki tare, sannan kuma akwai bukatar su sauya tsarin da suke amfani da shi, da haka wata kila a kawo karshen wannan rikicin kasarmu”.

Khassim Diagne, mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya a kasar, bayan gudanar da zanga-zangar ta Goma, ya ce ba za a lamunce irin wannan al’amarin ba.

A shekarar 1999 ne dai Majalisar Dinkin Duniya ta fara aike wa da jami’anta zuwa yankin gabashin kasar, a shekarar 2010 aka maida su masu aikin wanzar da zaman lafiya, inda suke da dakaru kusan dubu 16 da dari 3, sai dai Majalisar Dinkin Duniyar ta ce, akwai 230 daga cikin su da suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.