Ambaliyar ruwa ta kashe sama da mutum 20 a Jamhuriyar Nijar
Hukumomi a Jamhuriyar sun gargadi al'ummar kasar da su kara taka tsan-tsan, yayin da ambaliyar ruwa ta yi sanadin rayuwakn mutum 20, inda wasu 27 suka jikkata.
Wallafawa ranar:
Hukumomin bada agajin gaggawa sun ce daga lokacin da aka fara samun saukar ruwan sama a wannan shekara an samu asarar tarin dukiyoyi, baya ga asarar rayuka da dama.
Wannan na zuwa ne yayin da masu rajin kare muhalli ke gargadin gwamnatocin kasashe, kan illolin da ke tattare da matsalar sauyin yanayi, ciki kuwa har da ambaliyar ruwa, wanda tuni aka fara ganin hakan a kasashe da dama.
Alkalumman da mahukunta suka fitar a Jamhuriyar Nijar, sun ce ambaliyar ta bana, kawo yanzu ta shafi mutane sama da dubu 48, yayin da daruruwan dabbobi suka mutu, kamar dai yadda ambaliyar ta shafi makarantu, wuraren ibada, da kuma rumbuna ajiye abinci a sassa da dama na kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu