Hukumar zaben Senegal ta shiryawa zaben yan majalisu na gobe lahadi
An kawo karshen yakin zaben yan majalisu na kasar Senegal, zaben da za a yi gobe lahadi 31 ga watan yuli a wani lokaci da yan siyasa musaman bangaren adawa ke kokawa ganin yada shugaban kasar Macky Sall ke tafiyar da shugabanci.
Wallafawa ranar:
Kujeru 165 ne yan siyasar kasar daga jam'iyyu takwas za su nemi lashe wa.
Zaben dake a matsayin zakaren gwajin dafi ga Shugaban kasar Macky Sall,da tarin yan kasar ke kallon sa a matsayin wanda ya gaza wajen magance matsallolin da suka hada da tsadar rayuwa,rugujewar inci fada aji.
Yan siyasa bangaren adawa sun shirya kam a wannan zabe na ganin sun samu rijaye a zauren majalisar,wata hanyar tilastawa shugaban kasar canza salon siyasa da kuma damawa da yan adawa a shugabancin kasar ta Senegal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu