Isa ga babban shafi

Tattalin arzikin Najeriya ya kama hanyar rushewa - Masana

Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewar tattalin arzikin Najeriya na gaf da durkushewa, sakamakon rugujewar asusun ajiyar kasar na kasashen ketare, da kuma kashe triliyan kusan 6 wajen shigar da kayayyaki a cikin watanni 3 na wannan shekara.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele
Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emefiele venturesafrica
Talla

Yayin da kasar ke fuskantar zabe mai zuwa, matsalolin da suka shafi tattalin arzikin na ci gaba da daukar hankali, musamman abinda ya shafi tsadar rayuwar jama’a da hauhawan farashin kayan masarufi da kuma na kayan more rayuwa.

Takaddama tsakanin Gwamnan Babban Bankin kasar da kuma kamfanin NNPC dake samarwa kasar makudan kudaden shiga daga kasashen waje, ya dada zafafa matsalar, inda babban bankin ya zargi kamfanin man da kin zuba kudaden da yake sayar da mai a kasashen duniya, yayin da kamfanin yace a watanni 6 na wanann shekarar ya zuwb Dala biliyan biyu da miliyan 700.

Binciken da Jaridar Premium Times ta gudanar yace a watanni uku na wannan shekara, Najeriya ta kashe naira triliyan biyar da miliyan dubu 900 wajen shigar da kayayyakin da ake bukata daga kasashen ketare, yayin da kudin da ake da shi a asusun ajiyar kasar na kasashen ketare na Dala biliyan 15 ba zai iya daukar nauyin bukatun kasar na watanni 4 ba.

Yanzu haka Najeriya tana fuskantar matsalar samun kudaden kasashen ketare musamman ga kamfanoni da yan kasuwar dake bukatar su domin shigar da kaya cikin gida.

Masanin tattalin arziki Dakta Kasim Garba Kurfi, ya shaidawa RFI Hausa cewar gazawa wajen fitar da ganga kusan miliyan biyu na mai, da kasar ke yi tare da raguwar kudaden da 'yan Najeriya suke aikewa gida da kuma karancin kayan da ake fita da su zuwa kasashen waje na daga cikin matsalolin da suke yiwa tattalin arzikin kasar barazana.

Alkaluma sun nuna cewar tsakanin watan Janairu zuwa Afrilun wannan shekara, gwamnatin Najeriya ta samu kudaden shigar da suka kai naira tiriliyan guda da biliyan 63, yayin da kudin bai kai kudin bashin da kasar ke biya ba na naira tiriliyan guda da biliyan 94 saboda rarar naira biliyan 300 dake tsakanin su.

Dakta Kurfi yace ya zama wajibi gwamnati da jama’ar kasar su sake fasalin tafiyar da kasar, wajen rage dogaro da kayayyakin da ake shiga da shi daga kasashen ketare da kuma bunkasa ayyukan kamfanonin cikin gida da kuma harkar samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.