Isa ga babban shafi

Sojin hayar Rasha ke da hannu a kisan fararen hula a Mali- MDD

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa Sojin Mali da taimakon wasu Sojoji farar fata ne suka taka muhimmiyar rawa wajen kisan fararen hula 33 a yankin Segou gab da kan iyakar kasar.

Yankin Menaka na kasar Mali da ke fama da matsalar ayyukan ta'addanci.
Yankin Menaka na kasar Mali da ke fama da matsalar ayyukan ta'addanci. © AFP PHOTO / Etat Major des Armees
Talla

Cikin watan Maris din da ya gabata ne aka gano gawar wasu ‘yan Mauritania 29 da ‘yan Mali 4 a kauyen Robinet El Ataye da ke yankin na Segou wadanda bayanai ke cewa tun a ranar 5 ga watan ne Sojojin suka kame mutanen 33 bayan lakada musu duka.

Rahoton kwararrun na Majalisar Dinkin Duniya da ya fita a karshen watan jiya kuma AFP ta wallafa a jiya, ya bayyana irin cin zarafi da kisan gillar da Sojoji ke aikatawa kan fararen hula a Mali.

Wata majiya diflomasiyya a New York ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa fararen fatar da ke jagorancin cin zarafin a Mali Sojojin hayar da kasar ta dauko daga Rasha ne na kamfanin Wagner.

A dan tsakanin da aka samu kisan fararen hular, rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya ce an rika samun matsalar bacewar mutanen da basu ji ba basu gani ba a kan iyakar Mali da Mauritania.

Mahukuntan Nouakchott sun zargi Sojin Mali da aikata laifukan ta’addanci kan al’ummar Mauritania akan iyaka ko da ya ke Mali ta musanta hannun Sojinta ko da ya ke Bamako ta musanta tare da neman hujjar da ke hannun Sojinta a kisan.

A tsakiyar watan Maris ne kasashen biyu suka kaddamar da wani shirin binciken kwa-kwaf kan yawaitar kashe-kashen ko da ya ke har zuwa yanzu basu kai ga fitar da rahoton binciken bas ai zuwa tsakiyar watan nan.

Kasashen yammaci na ganin Sojin hayar na Rasha ke da hannu a kisan fararen hular yayinda Bamako ke ganin Sojin na Wagner ke taimaka mata wajen tabbatar da tsaron kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.