Isa ga babban shafi

Fursunoni sama da 800 sun tsere daga gidan yarin Congo

Fiye da fursunoni 800 ne suka tsere daga wani gidan yari a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, bayan farmakin wasu ‘yan bindiga, inda suka kashe ‘yan sanda biyu.

Fursunoni kalilan suka rage a cikin gidaan yarin na Kakwangura
Fursunoni kalilan suka rage a cikin gidaan yarin na Kakwangura AFP - MICHEL LUNANGA
Talla

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kakakin rundunar sojin yankin Beni a Jamhuriyar Demokradiyar ta Congo, Kaftin Antony Mualushayi ya ce cikin daren Talata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan yarin Kakwangura da ke garin Mutembo.

Alkaluman farko sun nuna cewa,  ‘yan sanda biyu ne aka kashe, yayin da mahari guda ya gamu da ajalinsa.

Wata majiyar hukumar gidan yarin da ta nemi a sakaya sunanta ta ce, fursunoni 49 kacal suka rage cikin 872 da ke tsare kafin harin.

Kakakin sojin ya daura alhakin harin kan kungiyar Mai-Mai da ke dauke da makamai a gabashin Jamhuriyar Demokaradiyyar Congo.

Sai dai wata kungiyar KST da ke sa-ido kan rikicin kasar  mai cibiya a Amurka ta ce ‘yan tawayen ADF da ke alaka da IS ne suka kai harin, kamar yadda ta wallafa ta shafinta na Twitter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.