Isa ga babban shafi

Guinea ta rusa kawancen jam'iyyun da ke son mayar da kasar turbar demokradiyya

Gwamnatin mulkin sojin kasar Guinea ta sanar da rusa kawancen jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hular da ke gwagwarmayar da dawo da tsarin dimukuradiyya a kasar wato (FNDC).

Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kanal Mamady Dambouya, bayan wata ganawa da wakilin kungiyar ECOWAS a birnin Conakry.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Guinea, Kanal Mamady Dambouya, bayan wata ganawa da wakilin kungiyar ECOWAS a birnin Conakry. AFP - JOHN WESSELS
Talla

Sanarwar rusa kawancen na zuwa ne jim kadan bayan da gungun ya bukaci al’ummar Guinea su gudanar da zanga-zangar adawa da mulkin Sojin a ranar 17 ga wannan wata da muke ciki.

Kakakin gwamnatin kasar Ousman Gawal Diallo da ke bayar da dalilan rusa kawancen ya ce babu ta yadda za a bar wasu mutane su jefa kasa a cikin tashin hankali a fakaici, yana mai cewa ba wai su na kokarin tauye hakkin gudanar da zanga-zanga da doka ta bai wa jama’ar kasar ba ne, amma su na la’akari da halin kasar ta ke ciki a yanzu.

A cewar Diallo ko’ina a duniya, hakki ne a wuyan gwamnati ta rika yin la’akari da halin kasa ke ciki kafin bayar da damar yin zanga-zanga ko kuma shirya tarukan gangami.

Gwamnatin Sojin Guinea ta kafa hujja da irin abubuwan da suka faru lokacin haramtaciyyar zanga-zangar da kasar ta gani a kwanakin baya wadda ta kai ga asarar rayukan mutane 5, hakan ne a cewar gwamnatin ya tilasta musu hana bayar da damar sake fuskantar makamanciyarta.

Kakakin gwamnatin ta kasar Ousman Gawal Diallo ya ce ya kamata a fahimci cewa halin da kasar ta ke ciki yanzu ya sha bamban da na shekarun baya, saboda haka dole a dauki irin wannan mataki na hana tarzoma, kuma ana yin tarzoma ko kuma zanga-zanga ce idan an shiga yanayin da gwamnati ba ta sauraren jama’a, wanda kowa ya san ba haka lamarin ya ke  a kasar Guinea ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.