Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Mali ta maye gurbin firaminista Choguel Maiga

Majalisar sojin kasar Mali ta nada Kanal Abdoulaye Maiga a matsayin wanda zai maye gurbin firaministan farar hula Choguel Maiga da ke zaman jinya a asibiti.

Abdoulaye Maiga kenan
Abdoulaye Maiga kenan HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Matakin da ke zuwa  a wani lokacin da yan adawa ke zargin gwamnatin kasar da jefa Mali cikin bala’i.

Rundunar sojan Mali ta nada Kanal Abdoulaye Maiga a matsayin wanda zai maye gurbin firaministan farar hula na kasar na wucin gadi, wanda aka kwantar da shi a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Shi dai kanar Maiga shi ne mai magana da yawun gwamnati kuma ministan kula da yankuna da kuma hulda da hukumomi

Choguel Kokalla Maiga, mai shekaru 64, an nada shi a matsayin Firayim Minista bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Mayu 2021.

Tsohon Firaministan ya  kasance dan takarar da bai yi nasara ba a zaben shugaban kasa a shekarar 2002, 2013 da 2018.

Ya kasance mamba a kungiyar kawancen da ta kaddamar da zanga-zangar adawa da zababben shugaban kasar Mali, Ibrahim Boubacar Keita, kafin a hambarar da shi a shekarar 2020.

Maye gurbinsa da wani Kanar na nufin dukkanin manyan mukaman gwamnatin Mali biyu a halin yanzu suna hannun sojoji.

Shugaban mulkin soji, Kanar Assimi Goita ya nada kansa shugaban rikon kwarya bayan juyin mulkin watan Mayun 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.