Isa ga babban shafi

Congo na bincike kan dalilin sake bullar Ebola makwanni bayan kawo karshenta

Mahukuntan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na gudanar da bincike kan bullar cutar Ebola a gabashin kasar mai fama da rikici, kamar yadda hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana  ‘yan makwanni kalilan da sanar da kawo karshen annobar.

A karshen makon jiya aka sake samun bullar cutar ta Ebola a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
A karshen makon jiya aka sake samun bullar cutar ta Ebola a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. © AFP/Zoom Dosso
Talla

A farkon watan da ya gabata ne Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta sanar da kawo karshen cutar Ebola wadda ta bulla cikin kasar a baya bayan nan, sama da watanni 2 da barkewarta a lardin arewa maso yammacin kasar.

Akwai mutane 4 da aka tabbatar da sun harbu da wannan cuta, da kuma guda da ake zargin ya kamu, kuma dukkanninsu sun mutu, a lamarin da hukumar lafiya ta duniya ta bayyana a matsayin barkewar cutar karo na 14, tun da aka gano ta a shekarar 1976.

Wata sanarwa daga hukumar lafiya ta duniya ta ce yanzu hukumomin kasar na fargabar akwai yiwuwar wata mata mai shekaru 46 da ta mutu a ranar Litinin a arewacin lardin Kivu ta harbu da cutar, ganin cewa ta nuna alamun da ke da nasaba da cutar Ebola.

Gwamnatin kasar ta bukaci al’ummar kasar su yi taka tsan-tsan, tana mai cewa akwai dimbim alluran rigakafin wannan cuta a arewacin Kivu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.