Isa ga babban shafi

Ranar tunawa da wadanda suka bace: ICRC ta sanar da batan mutum dubu 64 a Afrika

Yau ce ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar da ake mayar da hankali akan mutanen da suka bata, inda kungiyar agaji ta ICRC ta ce a nahiyar Afirka kawai ana da mutane dubu 64 da suka bata.

Kungiyar ICRC na taka muhimmiyar rawa wajen sada iyalan da suka bace.
Kungiyar ICRC na taka muhimmiyar rawa wajen sada iyalan da suka bace. REUTERS/Omar Sanadiki
Talla

Alkaluman kungiyar sun bayyana cewar a Najeriya kawai akwai mutane sama da dubu 25 da suka bata, kuma kusan dubu 14 daga cikin su yara ne kanana.

Sanarwar da kungiyar ta gabatar ya danganta wannan matsala da tashe tashen hankulan da ake samu a nahiyar wadanda adadin su ya kai 35, ya kuma shafi dubban mutanen dake tserewa muhallin su domin tsira da rayukan su daga Yankin Meditereniya har zuwa kudu da sahara.

Darakatan tawagar kungiyar ICRC a Najeriya, Yann Bozon ya ce alkaluman yara dubu 14 da suka bata, ba shi ne ke bayyana irin matsalar da ake fuskanta ba, domin akwai wasu da dama da ba’a iya tantance sub a.

ICRC ta ce lokacin da yaran suka bar muhallin su, sun kan fuskanci matsaloli da dama da suak hada da tashin hankali da cin zarafi da dimuwa, abinda ke raba wasu da iyalan su baki daya.

Sanarwar ta ce ICRC na da alkaluman irin wadannan yara dubu 5 da 200 da suka bata, ba tare da sun san inda mahaifan su suke ba.

Kungiyar ta ce daga watan Janairu zuwa Yunin wannan shekara, ta taimaka wajen musayar bayanai tsakanin iyakai 1,250 da suka bata, yayin da ta sada 31 da yan uwan su, bayan samar da hanyar tintiba tsakanin wasu iyalai 440.

ICRC ta kuma ce wasu iyalai 377 sun samu bayanai dangane da 'yan uwan su da suka bata, sai kuma mutane 146 da aka taimaka wajen sauya tunanin su da taimaka musu ta bangaren tattalin arziki da bangaren shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.