Isa ga babban shafi

Boko Haram ta kashe masunta a yankin Tafkin Chadi

Mayakan Boko Haram sun yi awun gaba da masunta a Najeriya, inda suka kashe wasu yayin wani farmaki da suka kai yankin tafkin Chadi da ke jamhuriyar Nijar, a cewar wata majiyar tsaro.

Wasu mayakan Boko Haram.
Wasu mayakan Boko Haram. AFP
Talla

Arewa maso gabashin Najeriya dai na fuskantar rikicin mayakan jihadi na tsawon shekaru 13 da ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 40,000 tare da raba wasu kusan miliyan biyu da muhallansu tun daga shekarar 2009.

Kisan masuntan a wannan makon na nuna yadda rikici ya kunno kai a kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke makwabtaka da kasar, musamman a tsibiran tafkin Chadi da ke da dabarun yaki inda mayakan jihadi suka kafa sansanoni na boye.

Mayakan sun yiwa masunta da dama kawanya a tsibirin Kwatar Kaoulaha da ke yankin Diffa a ranar Lahadi zuwa litinin, inda suka kashe wasu tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin bin umarnin da aka ba su na barin yankin, kamar yadda wasu masunta suka shaida wa AFP.

“Masunta da dama ne mayakan Boko Haram masu biyayya ga Baakura Buduma suka kashe tare da yin garkuwa da wasu saboda rashin barin yankin kamar yadda aka umarce su,” inji Kallah Sani, yayin da yake bayani kan wani shugaban kungiyar Boko Haram na yankin.

Sani bai iya bayar da takamaimai adadin ba amma ya ce wadanda suka tsere sun shaida masa masunta da dama suna tsibirin a lokacin da aka kai harin.

Mutumin dai na daga cikin masunta kusan 300 da suka yi biyayya ga sanarwar barin aiki na sa’a guda, inda suka bar aikin da sauran dukiyoyinsu ga mayakan jihadi.

"Sun gaya mana cewa za su kwashe duk abin da muka mallaka a matsayin ganima tunda gwamnatinmu ta kwace musu kudadensu," kamar yadda ya shaida wa AFP.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne kungiyar Boko Haram ta umarci masuntan wadanda galibinsu ‘yan Arewa maso yammacin Najeriya ne da su fice daga yankin tare da barin dukiyoyinsu a matsayin ganima ga mayakan, inji wani masuntci, Anas Ibrahim.

“Masu tayar da kayar bayan sun dawo ne a ranar Lahadin da ta gabata inda suka kashe wadanda suka samu tare da lalata kwale-kwalen su na kamun kifi don hana su tserewa,” inji shi.

Tsibirin a matsayin mafaka

Hakazalika wata majiyar tsaron jamhuriyar Nijar ta tabbatar da faruwar lamarin da kuma kashe-kashen, inda ta ce 'yan bindiga sun harzuka da yadda Nijar ta kama masu kai musu abinci da wani mai safarar kudi.

Gwamnatin Nijar dai ba ta tabbatar da hakan ba har yanzu a hukumace.

Sai dai wani jami'in yankin ya shaidawa kamfanin dilancin labaran AFP cewa mayakan jihadin sun umarci mazauna yankin da su fice daga tsibiran tare da kashe wadanda ba su bi umarninsu ba.

Tafkin Chadi mai fadin fadama ya ratsa kan iyakokin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi, kuma masu jihadi sun yi amfani da kananan tsibiran da ke wurin a matsayin mafaka.

A shekarar 2014 ne kungiyar Boko Haram ta kwace tsibiran da ke tafkin Chadi bayan munanan hare-hare, lamarin da ya tilastawa masunta tserewa daga gidajensu.

Har yanzu dai kungiyar Boko Haram na rike da tsibiran da ke gefen tafkin na Nijar.

A shekarar 2020, kungiyar da ke ikrarin jihadi ta Yammacin Afirka wato, wacce ta balle daga Boko Haram, ta kwace mafi yawan yankunan da Boko Haram ke iko da su, tare da barin masunta su koma bisa yarjejeniyar za su biya kudaden haraji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.