Isa ga babban shafi

Yadda manyan mutane suka halarci bikin sunan jariran goggon biri a Ruwanda

Manyan jama'a da mashahuran mutane ne suka halarci bikin "kwita izina", taron sanya sunan jariran goggon biri da ke gudana kowace shekara a kasar Ruwanda.

A bana ne aka gudanar da irin wanna biki karo na 18, a kasarda ke tsakiyar Afirka.
A bana ne aka gudanar da irin wanna biki karo na 18, a kasarda ke tsakiyar Afirka. Getty Images/Vetta/Guenter Guni
Talla

Da yake magana daga Burtaniya, Yarima Charles yana daya daga cikin manyan jama'a da aka gayyata don sanya sunan jariran goggon birin.

"Jaririn da zan sakawa suna, namiji ne da aka haifa a ranar 29 ga Afrilu, 2022 daga gidan Umuhoza, ga mahaifiyarsa Agasaro. Sunan da zan ba shi shi ne Ubwuzuzanye wanda ke nufin jituwa", in ji Yarima Charles na Burtaniya.

Ubwuzuzanye na daga cikin jimlar goggon biri 20 na gandun dajin Volcano da ke arewa maso yammacin Ruwanda da aka radawa suna.

Wasu abubuwa da aka zabo da sunan birran sune wakilin mawakan Francophonie da mawakan Senegal Youssou N'dour.

"(Birina) An haife shi a ranar 8 ga Afrilu 2022 sunansa Turikumwe, wanda ke nufin muna tare. Kuma idan zai zo ya ziyarce ni a Faransa zan kira shi", in ji Louise Mushikiwabo, Sakatare Janar na kungiyar mawakan kasashen renon Faransa.

Mawakin Senegal Youssou N’dour, ya kara da cewa:

"Sunan da na ba ta shine Ihuriro, wanda ke nufin bada gudun mowa. An zabi wannan sunan ne don wakiltar Rwanda a matsayin cibiyar da ke da bangarori daban-daban."

A bana ne aka gudanar da irin wanna biki karo na 18, a kasar da ke tsakiyar Afirka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.