Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta bada tabbacin mika mulki ga fararen hula

Shugaban rikon kwarya a Burkina Faso, Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya ba da tabbacin mutunta  alkawurran da majalisar sojin kasar ta dauka na shirya zabuka tare da mika mulki ga farraren hula.

Laftanal-Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, kenan
Laftanal-Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, kenan AFP - LEONARD BAZIE
Talla

Shugaban Majalisar sojin Burkina Faso Laftana kanar  Damiba yayin  ganawa da takwaransa na Cote D’Ivoire Alassane Ouattara sun tattauna kan batutuwa da suka jibanci tsaron da kuma diflomasiya .

Paul-Henri Sandaogo na bayyana haka ne yayin wata ziyara da ya kai kasar Cote D’Ivoire bayan ziyararda ya kai kasar Mali.

Kungiyar kasashen yammacin Afirka ECOWAS da hukumomin Burkinabe sun amince a farkon watan Yuli kan batun mika mulki ga farraren hula  bayan watanni 24 na rikon kwariya.

Yayin amsa tambayar manema labarai game da  rawar da ya taka don kubutar da sojojin Cote D’Ivoire da ake tsare da su a Mali tun farkon watan Yuli, Paul Henry Damiba ya nuna cewa yana fatan a tabbatar da cewa an samu mafita daga hukumomin Mali da na Cote d'Ivoire..

An sako mata uku daga cikin sojojin 49  da ake tsare da su a Mali  ranar Asabar din da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.