Isa ga babban shafi

MDD ta kadu kan yadda ake samun yawaitar fyade a Najeriya

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa akan yadda ake samun karuwar aikata fyade a Jihar Adamawa dake Najeriya, inda ta bayyana cewar daga cikin fyade 5,000 da ake samu, 10 kacal ake hukunta wadanda suka aikata saboda rashin samun wadanda zasu bada shaida.

Fyade na cikin manyan abubuwan da ke cutar da rayuwar mata
Fyade na cikin manyan abubuwan da ke cutar da rayuwar mata © firstpost
Talla

Ulla Mueller, wakiliyar Asusun Hukumar dake kula da yawan jama’a na UNFPA a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya ta bayyana haka lokacin wajen taron dake tantance alkaluman aikata laifuffukan.

Mueller tace sun kaddamar da dakin binciken kimiya a Asibitin koyarwar Jami’ar Modibbo Adama dake Yola, wanda zai bada damar yin gwaji ga duk wanda aka yiwa fyaden domin gabatar da shaida a kotu.

Masanin harkar binciken likitan, Dr Kizzle Shako ta bukaci hadin kai domin fadakar da jama’a muhimmancin amfani da dakin binciken kimiyar domin samun shaidun da ake bukata dan gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.