Isa ga babban shafi

Rikici ya barke a Guinea, shekara guda bayan juyin mulkin sojoji

Shekara guda bayan juyin mulkin da soji suka gudanar a kasar Guinea, yau anyi arangama tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zangar adawa da sojoji a birnin Konakry.

Rikici ya barke a Guinea, shekara guda bayan juyin mulkin sojoji
Rikici ya barke a Guinea, shekara guda bayan juyin mulkin sojoji (Photo : Reuters)
Talla

Wannan sabuwar zanga zangar da akayi a wajen birnin na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekara guda da juyin mulkin da ya kawar da shugaba Alpha Conde daga karagar mulki.

Jagoran mulkin sojin Kanar Mamady Doumbouya yayi alkawarin mika mulki ga zababiyar gwamnatin farar hula bayan shekaru 3, amma 'yan adawa na ganin cewar lokacin yayi tsayi.

Gamayyar kungiyoyin jam’iyyun siyasar kasar ta kira zanga zangar ta yau domin bukatar sojojin su taikata lokacin da suka diba na mika mulkin.

Rahotanni sun ce duk da haramta zanga zangar da sojojin suka yi a watan Mayu da rusa kawancen kungiyoyin da ake kira FNDC a watan jiya, jama’a sun gudanar da zanga zangar jifa jifa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.