Isa ga babban shafi

Kamaru ta girke zaratan sojoji a yankin 'yan aware

Shugaban Kamaru Paul Biya ya bada umurnin girke zaratan sojin kasar a yankin 'yan aware da ke fafutukar kafa kasa ta kansu, wadanda ke amfani da Turancin ingilishi.

Wasu daga cikin sojojin Kamaru.
Wasu daga cikin sojojin Kamaru. © AFP - STRINGER
Talla

Rahotanni sun ce, wata wasika da Sakatare Janar na fadar shugaban kasa ya rubuta wa Ministan Tsaro, ta ce shugaba Biya ya amince da bukatar tura sojojin na musamman a Kudu maso Yamma da Arewa maso Yammacin kasar.

Wasikar ta ce, amincewar shugaban ta biyo bayan bukatar haka da Ministan Tsaro ya gabatar wa shugaba Biya, sakamakon fafatawar da ake yi tsakanin sojoji da 'yan awaren da ke dauke da makamai.

Tun a shekarar 2016 aka fara rikicin 'yan aware a kasar, sakamakon korafin da lauyoyi da kuma malaman makarantu suka gabatar inda suke zargin cewar ana nuna musu banbanci.

Bayan kwashe shekaru 6 ana fafatawa tsakanin 'yan awaren da jami’an tsaro, an samu rasa rayukan daruruwan mutane daga kowanne bangare, cikinsu har da fararen hular da rikicin ya ritsa da su.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta ce tashin hankalin ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 6,000, yayin da sama da dubu 600 suka rasa matsuguninsu, sama da dubu 77 kuma suka tsere zuwa Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.