Isa ga babban shafi

Ko me ya tilastawa makusantan shugaban Laberiya yin murabus?

Shugaban Laberiya George Weah ya amince da murabus din wasu makusantansa guda uku bayan da Amurka ta zarge su da cin hanci a watan da ya gabata. 

Shugaban Laberiya George Weah, kenan
Shugaban Laberiya George Weah, kenan AFP
Talla

Nathaniel McGill, tsohon ministan harkokin fadar shugaban kasa wanda ya rike mukamin shugaban ma'aikata na fadar shugaban kasa, da Bill Twehway, wanda ya jagoranci hukumar kula da tashar jiragen ruwa ta kasar, da Sayma Syrenius Cephus, lauyan Liberiya kuma babban mai shigar da kara, duk sun yi murabus, in ji sanarwar fadar shugabancin kasar.

Shugaban ya dakatar da mutanen daga ayyukansu ne a tsakiyar watan Agusta bayan da Washington ta kakaba musu takunkumi kan zargin cin hanci da rashawa da ke da alaka da kwangilar miliyoyin daloli da kuma akalla dala miliyan 1.5 da aka karkatar na gwamnati.

Wannan ya hada da almubazzaranci da kadarorin gwamnati, da wawure wasu kadarori na daban don amfanin kashin kai, da almundahana da suka shafi kwangilolin gwamnati ko hako albarkatun kasa, da sauransu.

Yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan alkawurran da George Weah ya dauka kafin hawansa mulki a shekarar 2018, sai dai yana tattare da kalubale wajen cika alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.