Isa ga babban shafi

An yi garkuwa da malaman darikar Katolika tare da kona coci a Kamaru

Wasu mahara da suka kona wani coci a yammacin Kamaru sun yi garkuwa da limaman coci guda biyar, mace daya da wasu masu kula da majami’ar mutum biyu, kamar yadda majami’ar Katolika ta bayyana.

Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin
Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin AFP/Reinnier Kaze
Talla

Wasu mutane dauke da makamai da ba a san ko su wanene ba ne suka kona cocin St Mary da ke kauyen Nchang a harin da aka kai ranar Juma’a, in ji taron limaman cocin na lardin Bamenda.

Har yanzu dai ba bu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, amma sau da yawa kungiyoyin ‘yan aware ne ke kai su, kuma su kan sa a sako mutanen da aka yi garkuwa da su bayan neman kudin fansa ko tattaunawa da shugabannin yankin.

Yankunan Arewa maso Yamma da kuma Kudu maso Yamma na kasar Kamaru sun sha fama da rikicin da ya barke tsakanin ‘yan awaren anglophone da kuma gwamnatin kasar tsawon shekaru.

Masu magana da harshen Ingilishi su ne mafi yawan al'ummar yankunan kasar Kamaru mai magana da harshen Faransanci, wanda shugaba Paul Biya ke jan ragamar mulki tun shekara ta 1982.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 6,000 tare da raba kusan mutane miliyan guda da gidajen su, a cewar wata kungiyar masu fafutuka ta kasa da kasa.

Masu sa ido na kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya sun ce bangarorin biyu sun tafka cin zarafi da suka hada da aikata laifukan kan fararen hula.

A makon da ya gabata, an kashe mutane shida a wani hari da aka kai kan wata motar safa a yankin yammacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.