Isa ga babban shafi

Zanga-zangar adawa da mayakan M23 a Congo ta jikkata mutane da dama

Mutum guda ya mutu wasu biyu kuma sun jikkata a yankin gabashin kasar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, lokacin wata zanga zangar neman kawo karshen mamayen da mayakan kungiyar M23 suka yi wa yankin, kamar yadda majiyoyin Asibiti da kungiyoyin farar hula suka sanar.

'Yan kasar dai na neman kawo karshen mayakan M23
'Yan kasar dai na neman kawo karshen mayakan M23 REUTERS - STRINGER
Talla

Zanga-zanga da aka gudanar a Rutshuru, dake tsakkiyar yankin arewacin Kivu, ta gudana ne bisa kiran da kungiyoyin farar dake nuna rashin amincewa da mamayen da mayakan na M23 suka yi wa yankin, sama da kwanaki 100 a garin dake da matukar muhimmanci, inda ya hada kan iyaka da kasar Uganda.

Mahukumtan Kinshasa sun zargi Rwanda da taimakawa yan tawayen, zargin da Kigali ta musunta

Yanzu haka dai akwai tattaunawar da aka shirya yi bisa shawarar shugaban Faransa Emmanuel Macron a birnin New York daura da taron MDD, tsakanin shugaban  Congo Félix Tshisekedi da takwaransa na  Rwanda Paul Kagame, domin lalubo kawo karshen tayar da jijiyoyin wuyan da ake ci gaba da yi tsakanin kasshen biyu abokan juna.

A cikin jawabin da ya gabatar a gaban zauren MDD shugaban na Congo Félix Tshisekedi,  ya sake zargin kasar Rwanda da tursasawa ta fannin soji da kuma mamayen kasarsa, ta hanyar tallafin da mahukumtan Kigali ke baiwa kungiyar mayakan M23, tsohuwar kungiyar 'yan tawayen ta yan kabilar Tutsi da suka sake daukar makamai a karshen shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.