Isa ga babban shafi

An yi bikin cika shekaru 20 da hatsarin jirgin mafi ruwa muni a Senegal

Shekaru 20 bayan nutsewar jirgin Le Joola, a Senegal inda kusan mutum 1,900 suka mutu yau litinin ake bikin tunawa da wannan rana da ta kasance mafi munin gaske a kasar.

Kusan mutum 1,900 ne suka mutu a lokacin hatsarin jirgin ruwan
Kusan mutum 1,900 ne suka mutu a lokacin hatsarin jirgin ruwan AFP PHOTO
Talla

Lokacin da labarin ya bazu cewa jirgin ya kife a daren 26 ga Satumba, 2002, mutane da dama sun shiga dimuwa, musamman a kudancin kasar.

Kimanin mutane 1,863 ne suka nutse, wanda ya zarce adadin mutanen da bala'in Titanic ya kashe sama da 1,500 kimanin shekaru 90 da suka gabata.

Jirgin ruwan Le Joola ya yi taho-mu-gama ne a gabar tekun Gambiya lokacin da yake kan hanyar Ziguinchor zuwa Dakar babban birnin kasar.

Jirgin ruwan ya taka rawar gani sosai a garin Casamance, inda ya samar da hanyar rayuwa zuwa Dakar da jigilar kayan amfanin gona da kuma 'yan yawon bude ido.

Yankin Casamance, wanda ya raba Senegal da Kasar Gambiya, tun a shekara ta 1982 ta yi fama da tawayen 'yan aware.

Kungiyoyin wadanda abin ya shafa sun ce fiye da fasinjoji 2,000 daga kasashe fiye da goma ne suka mutu, kuma 65 ne kawai suka tsira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.