Isa ga babban shafi

Mayukan bilicin da ke sauya kalar fata na samun karbuwa a Kamaru- Bincike

Wani binciken kwararru a Kamaru ya nuna yadda mata suka rungumi dabi'ar amfani da mayukan bilicin don sauya kalar fatarsu, duk da yadda gwamnatin kasar ta haramta shigar da nau'in mayukan dai dai lokacin da masana ke gargadin game da illolin da ke tattare da ta'ammali da wadanan mayuka ga lafiyar dan adam.

Matsalar Bilicin na ci gaba da zama ruwan dare a sassan Kamaru duk da haramcin gwamnati kan ta'ammali da nau'ikan mayukan masu sauya kalar fata.
Matsalar Bilicin na ci gaba da zama ruwan dare a sassan Kamaru duk da haramcin gwamnati kan ta'ammali da nau'ikan mayukan masu sauya kalar fata. © RFI/Pearl Akanya Ofori
Talla

Tun cikin watan Agustan da ya gabata ne gwamnatin Kamaru ta haramta shigarwa da kuma shafa mayukan na bilicin da ke sauyawa ko kuma karawa fata haske a fadin kasar.

Masana harkokin lafiya dai sun jima suna gargadin mutane musamman mata da su ne kan gaba wajen shafe-shafen, kan su kauracewa wannan ta’ada, sai dai alamu na nuna cewa kiran baya samun shiga.

Ministan lafiya na Kamaru Dr Kwaku Agyeman Manu, a wata zantawarsa da wani gidan talabijin din kasar ya ce tun bayan sanar da matakin haramta shigo da mayukan na bilicin, ya na fuskantar barazana daga mata da 'ya'yan masu fada aji kasancewar su ne kan gaba wajen ta'ammali da nau'ikan mayukan na kara hasken fata.

A cewar ministan lafiyar, ba zai janye wannan mataki ba har sai hakarsu ta cimma ruwa, wajen dakile dabi'ar ta amfani da mayukan tsakanin al'ummar kasar.

Masana sun yi ikirarin cewa matsalar kai tsaye na shafar tattalin arzikin kasar lura da yawan jama’ar da ke amfani da mayukan.

A zantawar sashen turanci na RFI da wata mata ‘yar asalin Kamaru mai shekaru 63 da aka bayyana sunan ta da Jeanne, ta ce biris din da ta yi da kiran masana kiwon lafiyar ya sanya ta kamu da cutar daji ta fata.

A cewar dattijuwa Jeanne, babban tashin hankalin ta shi ne yadda mutane ke kyamar mu’amala da ita la’akari da yadda cutar ke haddasa fitar mugunya a jikinta duk kuma sanadin shafe-shafen mayukan kara hasken fatar da ta shafe tsawon shekaru 40 ta na yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.