Isa ga babban shafi

Ebola ta jefa tsarin kiwon lafiyar Uganda cikin dimuwa

Kungiyar agaji ta Red Cross a Uganda ta ce tsarin kiwon lafiyar kasar na fuskantar matsala yayin da adadin masu kamuwa da cutar Ebola ke karuwa.

Hukumomin lafiya na cikin fargabar yaduwar cutar a sassan kasar
Hukumomin lafiya na cikin fargabar yaduwar cutar a sassan kasar RFI
Talla

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce akalla mutane tara ne suka mutu a halin yanzu sakamakon kamuwa da cutar, ciki har da likita, kuma akwai jimillar mutane 43 da aka tabbatar sun kamu da cutar tun bayan sanar da bullar Ebola a ranar 20 ga watan Satumba.

Ebola na haifar da mummunar illa a jikin dan adam, wanda galibin wadanda suka harbu da cutar na mutuwa idan basu samu kulawar gaggawa ba. Cutar kamar yadda masana kiwon lafiya suka tabbatar tana da saurin yaaduwa, abin da ya sa aka ayyana ta a matsayin cuta mai barazana ga rayuwar mutum.

Daraktan sadarwa na kungiyar agaji ta Red Cross a Uganda, Irene Nakasiita, ta yi nuni da cewa barkewar cutar ta Ebola ta zo ne kai tsaye bayan barkewar cutar  COVID-19, da sauran bala'o'i, tare da kawo kaulbale mai girma ga ayyukan kungiyar.

“Duba da abubuwan da ake bukata da kuma tsammanin al’umma, hakika ya fi karfin karfin halin da ake ciki a halin yanzu,” in ji Nakasiita.

Yayin da muke duban tabbatar da lafiyarmu ta hanyar ba kanmu kariya da sauran matakan da suka dace na yakar cutar, dole ne mu tallafa wa al'ummomin, "in ji ta.

Taimakawa hukumomin lafiya na Uganda

Kungiyar ita ce kan gaba wajen kwashe marasa lafiya da ake zargin suna dauke daga cutar daga cikin al’umma, domin killace su, wadanda suka mutu kuma ana musu jana’iza ta musamman.

"Har sai an bayyana Uganda a matsayin kasar da ba ta da cutar Ebola, ba za mu iya yin alkawarin cewa hakan zai kawo karshen wannan cut aba daga nan zuwa Disamba ko Janairu ko Mayu ko Maris ba,"  'Amma dole ne mu ci gaba da tattara bayanai don mu samu damar yin aiki tare, amma mafi girman kawo karshen kalubalen shine a matakin al'umma," in ji Nakasiita.

Yayin da kasar ke cikin shirin ko-ta-kwana, Hukumar Lafiya ta Duniya ta lura a makon da ya gabata cewa, an fara gano bullar cutar a tsakanin wasu manyan mutane masu karfin fada aji, lamarin da ya sanya fargabar yaduwar cutar zuwa babban birnin kasar da kuma kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.