Isa ga babban shafi

Mayakan ADF sun kashe fararen hula 13 a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

Gungun mayakan da ake zargin na kungiyar ADF da ta yi kaurin suna ne, sun kashe akalla mutane 13, ciki har da sojojin gwamnati uku, a wani hari da suka kai a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Mayakan ADF a Jamhuriyar Congo.
Mayakan ADF a Jamhuriyar Congo. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

Mayakan sun kai harin ne a garin Beu-Manyama da ke yankin Beni a daren Lahadin da ta gabata, kamar yadda mazauna garin suka bayyana.

Shugaban kungiyoyin fararen hula na yankin Kinos Katuo ya ce adadin mutane 13 da aka bayyana sun mutu a harin na kungiyar ADF na wucin gadi ne.

Wani mai magana da yawun rundunar sojin Jamhuriyar Congo da kamfanin dillancin labaran AFP ya tuntuba ya ki cewa komai, amma ya yi ishara da wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Lahadin da ta gabata wadda ta ce sojojin sun yi arangama da ‘yan ta’adda masu dauke da makamai a yankin, inda suka kashe uku daga cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.