Isa ga babban shafi

Wasu hotunan bogi sun nuna yadda Faransa ke daukar nauyin ta'addanci a Mali

Wasu hotunan bogi da bidiyo da ake yadawa a shafukan sada zumunta sun nuna hujjojin da ke tabbatar da yadda Faransa ke daukar nauyin ayyukan ta’addancin a yankin Sahel musamman kasar Mali da a baya-bayan nan aka samu farraka tsakaninta da Paris.

Wasu 'yan ta'adda a Mali.
Wasu 'yan ta'adda a Mali. Reuters
Talla

Tashar France24 da ta wallafa labarin yau alhamis ta ce wasu kafofi mallakin kungiyoyin da ke kin jinin Faransa da masu goyon bayan Rasha da Sojin haya na Wagner ne suka fitar da wasu hotuna hade da bidiyo dukkaninsu marasa tushe wadanda ke zargin hannun Faransar a daukar nauyin ta’addanci a Mali.

Bidiyon da kungiyoyin suka wallafa a Youtube ya tattaro mabanbantan hotuna da ke ikirarin hannun Faransar a daukar nauyin ta’addanci, ciki har da bidiyon wasu sojoji Faransawa na bayar da makamai ga ‘yan ta’adda.

Sai dai wani dogon sharhi da kafar talabijin ta France24 ta yi game da hotuna da kuma bidiyon ta fito da hakikanin bidiyon wanda ke nuna yadda sojojinta ke tattara makamai don yakar ‘yan ta’adda a kasar ta Mali.

Galibin hotunan da aka yi amfani da su a wannan ikirarin sun kunshi hotunan kamfanin AP mallakin Faransa wadanda aka sauya fasalinsu da nufin gamsar da mutane cewa Faransa ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.