Isa ga babban shafi

Dubban 'Yan kasar Mali sun yi zanga-zangar adawa da batanci ga musulunci

Dubban al’ummar Mali ne ke ci gaba da zanga-zangar nuna adawa da wani faifan bidiyon batanci ga addinin Islama zanga-zangar da majalisar kolin addini ta kasar ta tsara gudanarwa tun daga ranar juma’a.

Dubban masu zanga-zangar goyan bayan mulkin sojin Mali a Bamako 14/01/21.
Dubban masu zanga-zangar goyan bayan mulkin sojin Mali a Bamako 14/01/21. AP - Harandane Dicko
Talla

Duk da cewa tuni gwamnatin Sojin kasar ta yi tir da bidiyon wanda ke yawo a shafukan sada zumunta da ke matsayin keta hadi ga littafi mai tsarki, amma al’ummar kasar ta Mali na ci gaba da nuna fushinsu kan fitar bidiyon tare da bukatar gaggauta hukunta masu hannu a fitarsa.

Mali wadda kashi 95 na al’ummarta mabiya addinin Islama ne, mutane fiye da miliyan guda ne suka faro gangamin wanda suka ce dole gwamnati ta shar’anta dokar mutunta addinin Islama, da annabin rahama da kuma littafi mai tsarki.

Ofishin mai gabatar da kara na Bamako ya bayyana cewa, an tsare mutane shida da zarginsu da hannu wajen yada faifan bidiyo da ke nuna wani mutum yana yin kalaman batanci da cin mutuncin addinin musulunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.