Isa ga babban shafi

Shekaru 40 da darewar Paul Biya kujerar shugabancin Kamaru

A jiya lahadi,  Paul Biya ya cika shekaru 40 da darewa kan karagar shugabancin kasar Kamaru, abin da ke nuni da cewa shi ne shugaba na biyu mafi dadewa kan karagar muki a nahiyar Afirka.Duk da cewa shugaban, mai shekaru 89 a duniya bai fito bainar jama’a ba a jiya,  magoya bayansa sun gudanar da kasaitaccen biki a birnin Yaounde domin taya shi murna.

Shugaban Kamaru, Paul Biyaa.
Shugaban Kamaru, Paul Biyaa. AFP/File
Talla

Paul Biya mai shekaru 89 a duniya, yanzu haka dai yana kan wa’adin mulkinsa karo na 7 ne a jere, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya bayar da damar hakan.

Wannan dai na nuni da cewa a cikin shekaru 62 da samun ‘yancin-kai, duka duka Kamaru ta samu shugannin biyu ne, wato Ahidjo sai kuma Paul Biya.

Domin murnar cikarsa wadannan shekaru kan karaga, a jiya lahadi a rassa 360 na jam’iyyar RDPC ciki da wadda shugaban ya kafa tun a 1985, an gudanar da manyan shugulgula.

A yanzu haka dai Paul Biya, shi ne shugaba na biyu mafi dadewa kan karagar mulki a Afirka baya ga takwaransa na Equatorial Guinea Teodero Obieng Nguema.

Yayin da magoya bayan shugaban ke jinjina masa saboda yadda Kamaru ke ci gaba da rike matsayinta na kasa mafi karfin tattalin arziki a yankin Tsakiyar Afirka, masu hamayya da shi kuwa, na zargin gwamnatinsa da tauye hakkin bil’adama da kuma gaza tunkarar matsalolin tsaro a yankunan ‘yan aware masu amfani da turancin Ingilishi ko kuma yakin da kasar ke yi da ayyukan Boko Haram.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.