Isa ga babban shafi

Shugaban gwamnatin sojin Chadi ya nada 'yan majalisar dokoki 100

Shugaban rukon kwaryar kasar chad Janar Mahamat Idriss Deby Itno  ya nada karin mutane 104 a matsayin wakilai a cikin zauren majalisar dokokin kasar, kamar dai yadda ya dauki alkawari bayan kammala taron tattauna matsalolin kasar da aka yi a birnin Doha na kasar Qatar.

Jagoran gwamnatin sojin chadi  Mahamat Idriss Deby.
Jagoran gwamnatin sojin chadi Mahamat Idriss Deby. AFP - BRAHIM ADJI
Talla

Taron saita alkiblar kasar  wanda ya gudana a watan da ya gabata ya ba da shawarar kara yawan mambobin majalisar wucin gadin, da ke aiki a matsayin majalisar dokoki, daga 93 zuwa 197.

A cikin kudurin dokar da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya gani, Janar Deby ya nada “karin mambobin majalisar ‘’CNT” 104, wadanda suka hada da tsoffin ‘yan jam’iyyar adawa, da ‘yan tawayen da suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a watan Agusta da kuma wakilan kungiyoyin farararen hula.

To amma duk da haka, akwai wasu 'yan adawa da kungiyoyin 'yan tawaye da suka kauracewa taron saita alkiblar kasar, inda suke nuna rashin amincewarsu.

Janar din mai shekaru 38 ya karbi ragamar mulki a watan Afrilun 2021 bayan an kashe mahaifinsa, wanda ya yi mulkin Chadi tsawon shekaru 30 a lokacin da ya jagoranci rundunar sojin kasar don kai farmaki kan 'yan tawaye .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.