Isa ga babban shafi

Dakarun Congo na ruwan bamai bamai kan 'yan tawaye a gabashin kasar

Mayakan ‘yan tawayen M23 na ci gaba da matsawa zuwa birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, yayin da a hannu daya ‘yan tawayen suka yi ikirarin kama birane da dama ciki har da Kibumba da ke lardin Nyira-gongo.

Sojojin Congo da na Majalisar Dinkin Duniy a gabashin kasar. 2014
Sojojin Congo da na Majalisar Dinkin Duniy a gabashin kasar. 2014 MONUSCO/Abel Kavanagh
Talla

A zuwa marecen wannan alhamis dai an ci gaba da fada tsakanin ‘yan tawayen da kuma dakarun gwamnati ne a yankin Nyira-gongo a wurin da bai wuce tazarar kilomita 20 ba a arewacin Goma, kuma mutanen da ke samun mafaka a sansanin ‘yan gudun hjira da Kanyaruchinya sun tabbatar da jin karar harbe-harbe daga yankin.

Wasu shaidun kuwa sun tabbatar da cewa wani jirgin Congo ya kai hare-hare ta sama akalla sau biyu kan mayakan na M23 kusa da garin Kibumba, yayin da fararen hula da suka samu kansu a cikin yanayi na firgita ke ci gaba da tserewa domin barin yankin.

Ofishin hukumar kula da ayyukan jinkai ta MDD wato Ocha a yankin Arewacin Kivu, ta ce adadin mutanen da suka gudu suka bar yankin da ake wannan fada ya zarta dubu 262, kuma dukanninsu na cikin yanayi na galabaita saboda lokacin da suka dauka suna tafiyar kafa.

Daga cikin wadanda ke rayuwa a matsayin ‘yan gudun hijira har da yara kanana, kuma sama da 300 daga cikinsu ba sa tare da iyayensu a wannan tafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.