Isa ga babban shafi

An kashe mutane fiye da dubu 7 cikin watanni 3 a Afrika ta kudu- rahoto

Wasu sabbin alkaluma da rundunar ‘yan sandan Afrika ta kudu ta fitar sun nuna yadda aka kashe mutanen da yawansu ya haura dubu 7 a sassan kasar, wanda ke nuna karuwar laifuka da tashe-tashen hankula a kasar.

Wani yanki da aka kashe mutane a Afrika ta kudu.
Wani yanki da aka kashe mutane a Afrika ta kudu. AFP - IHSAAN HAFFEJEE
Talla

Rahoton da rundunar ‘yan sandan ta mikawa kwamitin majalisar kasar mai kula da laifuka a jiya laraba, ya nuna yadda aikata laifuka ya kai kololuwa tsakanin 1 ga watan Yulin da ya gabata zuwa 30 ga watan Satumba.

Rahoton ‘yan sandan ya bayyana cewa an samu karuwar aikata laifuka da kashe-kashe da akalla kashi 14 idan akwa kwatanta da yawan mutanen da aka kashe a irin lokacin cikin shekarar da ta gabata.

A irin wannan lokaci cikin shekarar 2021 makamantan tashe-tashen hankulan da rikice rikice da kuma kashe-kashen babu gaira babu dalili ya kai ga mutuwar mutane dubu 6 da 163 adadin da bai kai yadda aka samu a bana ba.

Akalla mata dubu guda ke cikin wadanda aka kashe cikin watannin 3 a Afrika ta kudu yayinda aka ci zarafin matan da yawansu ya haura dubu 13 sai kuma wasu dubu 1 da 277 da aka nufaci kashe su amma suka kubuta da kyar.

Rahoton rundunar ‘yan sandan ya nuna yadda aka yi garkuwa da mutanen da yawansu ya haura dubu 4000 cikin watannin 3 alkaluman da ke nuna yadda laifukan garkuwa suka karu da fin kashi 100 idan an kwatanta da bara.

Haka zalika laifukan cin zarafin mata da yara ta hanyar fyade ya karu da kashi 11 inda yanzu haka ake da kararraki fiye da dubu 10 gaban kotuna kan irin wadannan laifuka a sassan kasar cikin wannan lokaci.

Rahoton ya kuma bayyana yadda aka kashe yaran da yawansu ya kai 550 daga watan Aprilu zuwa Satumban shekarar nan a kasar ta Afrika ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.