Isa ga babban shafi

An baiwa hamata iska a majalisar dokokin Senegal kan cin mutuncin wani Shehu

‘Yan Majalisar Dokokin Senegal sun yi arangama da juna a zauren majalisar, inda suka yi ta musayar naushe-naushe da jefe-jefe da kujeru sakamakon zagin wani shehun Malami a kasar.

Majalisar Dokokin Senegal
Majalisar Dokokin Senegal © Senegal assembly twitter
Talla

Rikcin ya soma ne bayan wata ‘yar majalisa mai suna Amy Ndiaye daga jam’iyya mai mulki, ta furta wasu kalaman batanci ga wani Shehun Malami a kasar wanda ke nuna goyon bayansa ga bangaren ‘yan adawa.

'Yar majalisa ta sha mari

Bayan furucin nata, Ndiaye ta ji saukar mari a kuncinta daga wani dan majalisar daban na jam’iyyar adawa, yayin da ita ma ta yi ta maza ta jefe shi da kujera, sai dai ta fadi kasa, amma takwarorinta suka taimaka suka daga ta.

Kafin ka ce kwabo nan take fada ya kaure tsakanin ‘yan majalisar, amma daga bisani shugaban majalisar ya rushe taron zamansu na ranar Alhamis.

Fadan ya kaure ne a yayin kada wata kuri’a game da amincewa da kasafin kudin Ma’aikatar Shari’ar kasar na 2023.

Shehun Malami

Shehun Malamin mai suna Serigne Moustapha Sy da Ndiaye ta zaga, ba dan majalisa ba ne a Senegal, amma dai yana goyon bayan bangaren ‘yan adawa.

A ranar 27 ga watan Nuwamban da ya gabata, Ndiaye ta bayyana malamin a matsayin mayaudari, sannan mai nuna rashin ladabi ga shugaban kasar Macky Sall, yayin da ‘yan adawa suka tsaya kai da fata cewa, dole ne ta nemi afuwar malamin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.