Isa ga babban shafi

An gudanar da zanga-zangar kawo karshen rikicin 'yan tawayen Congo

An gudanar da zanga-zangar neman zaman lafiya da cocin Katolika ta shirya a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo a ranar Lahadi, domin nuna adawa da tashe-tashen hankula a gabashin kasar, kwanaki bayan kisan gillar da aka yi wa fararen hula.

Masu zanga-zangar adawa da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MONUSCO a Goma a ranar 26 ga Yuli, 2022.
Masu zanga-zangar adawa da tawagar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya MONUSCO a Goma a ranar 26 ga Yuli, 2022. AFP - MICHEL LUNANGA
Talla

Masu zanga-zangar dai sun yi ta rera taken bamaso ga munafuncin kasashen duniya" da kuma bamaso ga tsarin mulkin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo" a wani gangamin da aka gudanar a Kinshasa babban birnin kasar da sauran garuruwa.

Sai dai kuma an dakatar da wani tattakin da aka shirya gudanarwa a birnin Goma na gabashin kasar da ke kan iyaka da kasar Rwanda domin kaucewa yiwuwar kutsawa makwabciyar kasar.

Hukumomi sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon kisan gillar da ake zargin an yi wa fararen hula a gabashin kasar a makon jiya ya kai sama da 100.

Gwamnati dai ta zargi kungiyar ‘yan tawayen M23, wadanda suke ci gaba da haifar da tashe-tashen hankula tsawon watanni, da kashe-kashe a Kishishe, wani kauye mai tazarar kilomita 70 daga arewacin Goma.

Kungiyar ta M23 a karshen mako ta sake musanta cewa tana da alhakin kai harin, bayan da tuni ta kira zargin a matsayin mara tushe.

Sai dai shugabanta Bertrand Bisimwa a cikin wata sanarwa da ya fitar ya ce an kashe fararen hula takwas ta hanyar kuskurarren harsashi a yayin fadan da aka yi a kauyen ranar Talata.

M23, kungiyar 'yan tawayen Tutsi ce ta Congo wadda ta shafe shekaru da yawa ba tare da kai hare-hare ba, Sai dai watan Nuwambar bara ne ta sake daukar makamai tare da kwace garin Bunagana da ke kan iyaka da Uganda a watan Yuni.

Bayan wani dan kankanin lokaci da samun kwanciyar hankali, sai ta sake kai farmaki a watan Oktoba, inda ta kara fadada yankin da ke karkashinta sosai, ta kuma doshi Goma.

Kinshasa na zargin makwabciyarta Rwanda da baiwa kungiyar M23 goyon baya, lamarin da kwararrun Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin Amurka ma suka ja hankali a kai a 'yan watannin nan, sai dai Kigali ta musanta zargin.

Tattaunawar da aka yi tsakanin kasashen biyu a Luanda babban birnin kasar Angola, ta cimma yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 23 ga watan Nuwamba.

A ranar 25 ga watan Nuwamba ne dai aka shirya tsagaita wutar, ya kamata kuma bayan kwanaki biyu ne kungiyar ta M23 ta janye daga yankin da ta kwace, amma hakan bai samu ba.

Ita ma rundunar sojin Congo, ta zargi mayakan M23 da karya yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da dakarun gwamnati, zargin da kungiyar ke ci gaba da mus

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.